Isa ga babban shafi

Dakarun MINUSMA sun fara ficewa daga Mali

Dakarun rundunar kiyaye zaman lafiya a Mali sun janye daga sansaninsu na Aguelhhok a yankin Kidal mai fama da rikici, kamar yadda gwamnati sojin kasar ta bukata.

Taswirar kasar Mali
Taswirar kasar Mali © Studio graphique FMM
Talla

Janyewar dakarun na majalisar Dinkin Duniya da ake kira  MINUSMA dai ta janyo fargabar ta’azzarar rikici a yankin tsakanin dakarun  gwamnati da kungiyoyi masu dauke da makamai a game da iko da yankin.

A ranar Lahadi rundunar MINUSMA tayi korafin cewa rayuwar dakarunta na cikin hatsari, duba da yanayin janyewa da ta kira mara tsari daga sansanin Tessalit.

Tun ba yau ba dakarun sojin kasar ke ganin zaman MINUSMA ba shi da wani muhimmanci, illa dai kara lalacewar tsaro a yankin, mai tarin jama’a.

Bayanai na nuna cewa tun bayan juyin mulki sojojin ke bin hanyoyi da dama wajen raba gari da sojojin kasashen ketare musamman na Faransa da na majalisar Dinkin Duniya.

Ana dai ganin wannan mataki ba zai kara komai ba, illa ta’azzara matsalar tsaro, la’akari da yadda kungiyoyin aware da masu bore suka fara dawowa da ayyukan su, bayan ficewa daga yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla da su.

Mali na cikin kasashen yankin sahel da ke fama da ayyukan ta’addanci da sauran kungiyoyi masu dauke da makamai, lamarin da ya hallaka dubban rayuka da raba wasu miliyoyi da muhallan su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.