Isa ga babban shafi

An kashe dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali

Wani jami’in tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ya mutu a jiya Jumma’a a kasar Mali yayin da wasu takwas suka samu munanan raunuka sakamakon wani hari da aka kai a arewacin kasar mai fama da mayaka masu ikirarin jihadi.

Wani jami'an dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali, 9 ga watan Disambar shekarar 2021.
Wani jami'an dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali, 9 ga watan Disambar shekarar 2021. © AFP - FLORENT VERGNES
Talla

Cikin sanarwa da ta fitar da shafinta na Twiter MINUSMA tace an kwaiwa tagawar dakarun ne wani hari mai sarkakiya yayin da suke sintiri a kuda da garin Ber a yankin Timbuktu.

Sanarwar tace bayaga taka nakiya da aka binne da motar jami’an ta yi, an kuma bude musu wuta kai tsaye.

Rundunar ta ce wadanda harin ya rutsa da su sun fito ne daga wata runduna ta makwabciyarta Burkina Faso.

Shugaban MINUSMA El-Ghassim Wane ya yi Allah-wadai da harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.