Isa ga babban shafi

Harin kwanton bauna ya kashe jami'an MDD 3 a kasar Mali

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya 3 ne suka mutu yayin da wasu biyar suka samu munanan raunuka bayan wani harin kwanton bauna a tsakiyar kasar Mali.

Jami'an tsaro kenan lokaccin da suke kokarin kama wani dan kunar bakin wake a Bamako babban birnin kasar Mali.
Jami'an tsaro kenan lokaccin da suke kokarin kama wani dan kunar bakin wake a Bamako babban birnin kasar Mali. AFP - EMMANUEL DAOU
Talla

Wata sanarwa da MDD ta wallafa a shafin Twitter, ta ce dakarun wanzar da zaman lafiya na MINUSMA sun taka wani bam gefen hanya, abin da ya yi sanadin rayukan wasu daga cikin su.

Sanarwar ba ta bayya sunayen wadanda aka kashe ko kuma kasashen su ba.

Kasar Mali mai fama da talauci da ke tsakiyar yankin Sahel na yammacin Afirka, na fama da rikicin masu tayar da kayar baya na tsawon shekaru 1, abin da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane tare da tilastawa dubban mutane barin gidajensu.

An samar da rundunar MINUSMA, karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya tare da hadin gwiwar kasar Mali, a shekarar 2013.

Rundunar na da jami'an soji da 'yan sanda sama da 13,500, inda ta kasance daya daga cikin mafi girma amma kuma mafi muni a ayyukan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, wanda ke fama da dimbin hasarar rayuka, musamman sakamakon hare-haren bama-bamai.

A cikin watan Janairu, babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana a cikin wani rahoto cewa, dakarun wanzar da zaman lafiya 165 ne suka mutu, yayin da 687 suka samu raunuka a hare-haren wuce gona da iri tun watan Yulin shekarar 2013.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.