Isa ga babban shafi

Al'ummar Mali na zanga-zangar neman ficewar sojojin MDD da ke kasar

Daruruwan ‘yan kasar Mali ne suka gudanar da zanga-zanga a babban birnin kasar Bamako, inda suke bukatar sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya MUNISMA su fice daga kasar, ganin yadda su ka ce sun gaza wajen samar da zaman lafiya.

Sojojin Majalisar Dinkin Duniya na MINUSMA da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Mali.
Sojojin Majalisar Dinkin Duniya na MINUSMA da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Mali. AFP - SIA KAMBOU
Talla

Jam'iyyar Firaministan rikon kwarya Choguel Maiga da kungiyoyin farar hula masu goyon bayan gwamnatin mulkin sojan rikon kwaryar kasar ne suka shirya gangamin da aka gudanar a filin wasa na Palais des Sports.

Mutane da dama ne suka mutu a kasar sanadiyar hare-haren ‘yan ta’addan da ke da alaka da kungiyoyin ISIS da kuma al-Qaeda tun daga shekarar 2013.

A wannan shekarar ce kuma aka samar da rundunar MINUSMA da ke da sojoji sama da dubu 14, domin taimakawa sojojin kasashen waje da kasar da ke yaki da masu dauke da makamai, wanda kuma shine aikin wanzar da zaman lafiya mafi girma kuma mafi hadari a tarihin rundunar.

Sama da sojojin Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar dari 3 ne aka kashe.

A ‘yan watannin baya-bayan nan, ana yawan samun rikici tsakanin gwamnatin sojin kasar da kuma rundunar sojojojin MINUSMA, bayan da gwamnatin sojin Mali ke samun taimako daga sojojin hayar Wagner na Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.