Isa ga babban shafi

Amurka ta kakabawa shugaban kamfanin Wagner a Mali takunkumi

Amurka ta sanar da shirin kakaba takunkumin karya tattalin arziki kan shugaban dakarun kamfanin Wagner na Rasha a Mali, Ivan Maslov, wanda ta zarge shi da neman samun kayan aikin soji don amfani da shi a rikicin Ukraine.

Wani soja kenan da ke shiga ofishin Wagner a Rasha
Wani soja kenan da ke shiga ofishin Wagner a Rasha © REUTERS / IGOR RUSSAK
Talla

“Wadannan takunkumin da aka kakaba wa mutum mafi muhimmanci da ke jagorantar kungiyar Wagner a Mali na da nufin kawo karshen muhimman ayyuka na tallafawa ayyukan kamfanin,” in ji sanarwar.

Wadannan takunkumin sun hada da kwace dukkan kadarorin Ivan Maslov a Amurka, da kuma kamfanonin da ke da alaka kai tsaye da Mista Maslov, da kuma haramtawa kamfanonin da ke yankin Amurka gudanar da cinikayya tare da Mista Maslov.

Sanarwar fadar Amurka ta kuma kara da cewa kasantuwar kamfanin Wagner a Nahiyar Afirka wani karfi ne na kawo cikas ga duk wata kasa da bata da damar kawo karshen matsalar tsaro.

Wannan dai ba shi ne karon farko da aka sanya takunkumin kan kamfanin Wagner ko wasu jami’ansa ba, saboda ayyukan da yake gudanarwa a kasar Mali.

A karshen watan Fabrairu ne, Kungiyar  Tarayyar Turai ta ba da sanarwar jerin takunkumin da aka kakaba wa mutane goma sha biyu, ciki har da Mista Maslov, saboda zargin take hakkin bil'adama da aka danganta ga kamfanin.

Wagner, kamfanin da aka samar a shekarar 2014, Amurka na daukar ayyukan da dakarunsa ke yi a matsayin ta'addanci.

Amurka wacce ta kwashe shekaru da dama tana kokarin dakile tasirin Rasha a Afirka, tana zargin kamfanin na Wagner da take hakkin bil adama da kwace albarkatun kasa a nahiyar Afirka.

Wagner ya kafa kansa a matsayin babban mai taka rawa a rikicin Ukraine, musamman a yakin da ake yi a kusa da birnin Bakhmout, kuma an ga sojojin haya na kamfanin a kasashen Syria da Libya, kuma a baya-bayan nan a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, da kuma kasar Mali. .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.