Isa ga babban shafi

Burkina Faso ta goyi bayan Mali game da shirin murkushe masu dauke da makamai

Burkina Faso da ke karkashin mulkin soja ta bayyana goyon bayanta ga makwabciyarta Mali bayan wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da aka dade ana jira ya ce sojojin Mali da mayakan kasashen waje sun kashe akalla mutane 500 a wani farmakin ga masu tayar da kayar baya a shekarar 2022.

Tawagar dakarun Faransa kenan a wani kauye da ke Arewacin Burkina Faso
Tawagar dakarun Faransa kenan a wani kauye da ke Arewacin Burkina Faso © MICHELE CATTANI / AFP
Talla

Binciken da hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar, ya bayyana dalla-dalla yadda aka tara daruruwan mutane a garin Moura da ke tsakiyar kasar Mali a watan Maris din 2022 tare da harbe su.

Gwamnatin Burkina Faso ta ce ta yi mamakin abin da rahoton ya kunsa, tana bayyana hakan a matsayin abin da bashi da tushe.

Burkina Faso ta bayyana goyon bayanta ga gwamnatin kasar Mali, da ma dukkanin dakarun da ke yaki da miyagun dakarun da aka jibge a kasar ba bisa ka'ida ba, bisa zargin take hakkokin bil'adama, in ji ministan sadarwa Jean Emmanuel Ouedraogo a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Adadin mutanen da rahoton ya fitar ya nuna cewa danyen aiki ne da ya kasance mafi muni a kasar da ke yankin Sahel tun bayan barkewar rikicin masu dauke da makamai a shekara ta 2012.

Rahoton ya ce kusan mata 20 da kananan yara bakwai na daga cikin wadanda aka kashe, yayin da wasu bayanai ke nuni da cewa mata da 'yan mata 58 ne aka yi musu fyade da sauran nau'ikan cin zarafin mata.

Bangarorin biyu na Burkina Faso da Mali dai na karkashin mulkin soja ne da suka kwace mulki a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna fushi ga zababbun shugabanni kasashen, kan gazawar da suka yi na magance matsalolin da suka dabaibaye sha’anin tsaro.

Kasashen biyu dai sun yanke huldar soji da kasar Faransa wadda ke kawance da kasashen yankin Sahel, sannan kuma kasar Mali ta shigo da jami’an tsaron kasar Rasha domin tallafawa sojojinta.

Mali ta bayyana rahoton a matsayin shiryayye inda ta nanata cewa mutanen da ake zargin an kashe, masu tayar da kayar baya ne.

Rahoton na MDD bai bayyana sunayen kasashen da sojojin suka fito ba, amma Amurka ta dora alhakin kisan kan sojojin kamfanin Wagner na kasar Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.