Isa ga babban shafi

An rubuta Budaddiyar Wasika na neman kare aikin Jarida a Mali da Burkina Faso

Kafafen yada labarai da kuma kungiyar kare hakkin ‘yan jarida akalla 30 daga sassan duniya ne suka rattaba hannu kan wata budadiyar wasika, inda suke kira da a dauki matakan kare ‘yan jarida a Burkina Faso da kuma Mali.An dai wallafa wannan wasika ce a daidai lokacin da ake gudanar da bikin ‘yancin aikin Jarida a duniya da ake gudanarwa a wannan rana ta 3 ga watan Mayu. 

Kafafen yada labarai da kuma kungiyar kare hakkin ‘yan jarida akalla 30 daga sassan duniya ne suka rattaba hannu kan wata budadiyar wasika, inda suke kira da a dauki matakan kare ‘yan jarida a Burkina Faso da kuma Mali.
Kafafen yada labarai da kuma kungiyar kare hakkin ‘yan jarida akalla 30 daga sassan duniya ne suka rattaba hannu kan wata budadiyar wasika, inda suke kira da a dauki matakan kare ‘yan jarida a Burkina Faso da kuma Mali. © Studio graphique FMM
Talla

A wannan wasika, kungiyoyin da kuma kafafen yada labarai, sun bayyana fargaba a game da kisan ‘yan jarida, da wadanda ke bayyana ra’ayoyinsu, da hana kafaden yada labarai watsa shirye-shiryensu kamar dai RFI da kuma France 24, da tasa keyar wakilan wasu kafafen yada labaran Faransa Liberation da le Monde daga Burkina Faso, wadannan alamu ne da ke nuna cewa mahukunta na kokarin tauye hakkokin jama’a. 

Mali

A kasar Mali kuwa, wasikar ta yi nuni da yadda ake tursasawa ‘yan jarida da masu hankoran kare hakkin jama’a, inda a tsakanin watan Nuwamba zuwa Disambar shekarar da ta gabata, aka dakatar da tashar talabijin mai zaman kanta ta Joliba TV, yayin da a watan fabarairun bana, wasu suka lalata cibiyar ‘yan jarida ke Bamako. Kamar dai yadda aka cafke Ras Bath mai gabatar da shiri a wani gidan rediyo saboda ya bayyana takaici dangane da mutuwar tsohon firaminista Soumeylou Boubeye Maiga a hannun mahukuntan Mali. 

Saboda haka ne wadannan kungiyoyi da kuma kafafen yada labarai 30, ke nuna damuwa dangane da yawaitar hare-hare ko cin zarafin ‘yan jarida a Mali da Burkina Faso. 

Tauya hakkin 'Yan Jaridu

Ko a ranar 20 ga watan fabarairun wannan shekara, kwararren mai bincike na Majalisar Dinkin Duniya kan kare hakkin dan Adam Alioune Tine, ya fito fili karara inda ya bayyana fargaba dangane da tauye hakkin jama’a a Mali. 

Daga cikin kafafen yada labarai da suka rattaba hannu a wannan wasika har da dama daga Burkina Faso, sai kuma kungiyoyi da kafafen yada labarai na kasa da kasa da suka hada France 24, RSF, UPJ, Liberation, Wakat Sera, Cibiyar kare ‘yan jaridu ta Norbert Zongo, FIDH, Joliba TV News, Lefaso.net, Human Rights Watch da dai sauransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.