Isa ga babban shafi

Dubban Mata a Mali sun rungumi sana'ar man kadanya wajen dogaro da kai- rahoto

Kaso mai yawa na mata a Mali sun dogara da sana’ar sarrafa man kadanya wajen samun kudaden shiga ko kuma dogaro da kai dai dai lokacin da kasar ke kama hanyar zama jagora wajen cinikayya dama samar da nau'in man wanda ake fita da shi kasashe daban-daban.

Wasu Mata da ke sarrafa man kadanya.
Wasu Mata da ke sarrafa man kadanya. © RFI/Zubaida Mabuno Ismail
Talla

Yanzu haka dai Mali na matsayin jagora a wajen samar da man kadanyar biye da Najeriya ta biyu kana Burkina Faso, dai dai lokacin da a shekarun baya-bayan nan ake ganin karuwar bukatar nau’in man a kasashen duniya.

Musamman a yankunan karkara Mata a Mali na samar da nau'in man daga itaciyar kadanya don amfanin kansu da iyali gabanin fadaduwar sana'ar zuwa ta dogaro da kai.

Guda cikin ma’aikatun da ke samar da tsaftataccen man a Mali da aka kafa a shekarar 2003 karkashin jagorancin matan da ke sarrafa man, yanzu haka na dauke da ma’aikatan dindindin akalla dubu guda wadanda ke daukar albashin cfa dubu 54 dai dai yuro 70 a kowanne wata.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya shaida akwai kuma wasu dubunnan ma’aikata da ke aikin wucin gadi wadanda ake biyansu gwargwadon aikin da suka yi.

Alkaluman da kungiyar masu sarrafa man kadanya ta kasa da kasa ta fitar na nuna cewa akwai matan Afrika akalla miliyan 16 kama daga kasashen Senegal zuwa Sudan ta kudu da suka dogara da sana’ar man kadanyar musamman a yankunan karkara.

Bishiyar kadanya da ke matsayin fitacciyar itaciya a kusan dukkanin kasashen nahiyar Afrika bayan amfana da ‘ya’yanta a matsayin kayan marmari man da ake fitarwa daga jikinta ya shiga sahun mayuka mafiya daraja a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.