Isa ga babban shafi

Mali ta zargi rundunar MINUSMA da yi mata leken asiri

Gwamnatin mulkin sojin Mali ta bukaci masu gabatar da kara da su gudanar da bincike a kan rundunar kiyaye zaman lafiya ta  Majalisar Dinkin Duniya a a kan zargin leken asiri, biyo bayan rahoton rundunar da ya zargi dakarun Mali da kawayensu da yi wa fararen hula kisan gilla a shekarar da ta gabata.

Kanar Assimi Goïta, jagoran gwamnatin sojin Mali.
Kanar Assimi Goïta, jagoran gwamnatin sojin Mali. AFP - OUSMANE MAKAVELI
Talla

A wata sanarwa da aka wallafa a dandalin sadarwa a jiya Talata, ofishin mai gabatar da kara ya ce wani sashe da ya kware a kan yaki da ta’addanci  da masu aikata  laifuka na kasa da kasa ya samu korafi a kan aikin da rundunar MINUSMA ke yi a kasar.

MINUSMA ta gudanar da bincike a game da abubuwan da suka wakana a garin Moura na tsakiyar Mali a tsakanin ranar 27 zuwa 31 ga watan Mayu na shekarar 2022.

Kuma  rahoton da hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya ceakalla  mutane 500 ne dakarun Mali da mayaka daga kasashen waje  suka wa kisan gilla.

 Sanarwar korafin ta gwamnatin Mali ta bayyana rundunar Minusma  a matsayin masu hadin baki wajen aikata manyan laifukan da suka hada da leken asiri, kaarya gwiwar dakarun da ke yaki da ta’addanci da sauransu.

Kasar Mali na fama da matsalar tsaro sakamakon ayyukan ta’addanci da ya kunno kai a arewacin kasar fiye da shekaru 10 da suka wuce, lamarin da ya yi sanadin mutuwar da dama, ya kuma daidata tarin iyalai, kana ta bazu zuwa makwaftanta, Nijar da Burkina Faso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.