Isa ga babban shafi

Gwamnatin sojin Mali ta takura wa dakarun MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta koka kan yadda matsin lambar gwamnatin sojojin Mali ke jefa rayukan sojojinta na rundunar tsaron MINUSMA cikin hadari a daidai lokacin da suke ci gaba da ficewa daga kasar cikin hanzari. 

Sojojin Rundunar MINUSMA karkashin Majalisar Dinkin Duniya a Mali.
Sojojin Rundunar MINUSMA karkashin Majalisar Dinkin Duniya a Mali. © AFP / MARCO LONGARI
Talla

Bayanai sun ce, ko a cikin daren jiya, sai da ‘yan ta’adda suka kai wa tawagar Majalisar Dinkin Duniyar wadda ke kan hanyarta ta fita daga kasar hari, duk da dai babu wani asarar rai. 

Majalisar Dinkin Duniyar ta ce rashin hakurin da sojojin suka nuna wajen ba su damar shiryawa da kuma fita daga kasar a tsanake shi ne abin da ya haifar da wannan matsalar. 

Umarnin ficewar sojojin daga Mali ya kawo karshen shekaru 10 da suka kwashe suna aikin wanzar da zaman lafiya da fatattakar ta’addanci daga kasar da ke yankin saharar Afrika. 

Ana sa ran sojojin  fiye da dubu 15 za su kammala ficewa daga kasar zuwa ranar 31 ga watan Disamba mai zuwa. 

To sai dai kuma tuni bangarorin ta’addanci da ke kasar suka fara amfani da wannan dama wajen ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula da kuma yukurin kwace iko da wasu sassan kasar. 

Kungiyoyin ta’addanci masu alaka da kungiyar IS da kuma na ‘yan tawayen Tuareg su ne kan gaba wajen kai munanan hare-hare, duk da dai gwamnatin kasar ta sha musanta cewa harin nasu na fin karfin sojojinta. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.