Isa ga babban shafi

'Yan awaren Abzinawa sun sanar da kwace ikon arewacin Mali

‘Yan awaren Azbinawa na kasar Mali, sun sanar da yi wa arewacin kasar kawanya ta hanyar toshe manyan hanyoyin da suka hade sauran sassa da yankin, bayan da sojojin kasar suka ce an samu gagarumar nasara a cikin makwannin da suka gabata wajen yakar 'yan tawayen.

Dakarun kungiyar Ansar lokacin da suka yada zango a saharar Timbuktu ranar 24 ga Afrilu, 2012.
Dakarun kungiyar Ansar lokacin da suka yada zango a saharar Timbuktu ranar 24 ga Afrilu, 2012. © AP / STR
Talla

Kawancen kungiyar ‘yan tawayen ta ce ta yanke shawarar kafa shingaye a hanyoyin zuwa kan iyakokin kasar da kasashen Mauritania, Algeria da Jamhuriyar Nijar.

A cikin makwannin da suka gabata, kungiyar, wadda akasarin ‘yayanta ‘yan kabilar Abzinawa ne ta dandana kudarta a hannun dakarun Mali a tsakiyar watan Nuwamba, a lokacin da suka karbe iko da garin Kidal dake arewa maso gabashin kasar.

A watan Agusta ne fada tsakanin dakarun gwamnati da ‘yan awaren Abzinawa ya barke, bayan shekaru 8 rabon su da raba rana, sakamakon yadda dukkaninsu ke kokarin cike gurbin da janyewar dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dikin ta samar.

Rundunar kiyaye zaman lafiya da ake kira MINUSMA ta janye bisa bukatar gwamnatin mulkin sojin Mali wadda ta karbe mulki a shekarar 2020.

A cewar wasu ganau, mazauna yankin arewacin kasar, dakarun Mali sun samu taimakon sojin hayar Wagner na Rasha, amma gwamnatin kasar ta musanta kasancewar wasu sojojin haya a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.