Isa ga babban shafi

Sojojin Mali sun gano makeken kabari a Kidal bayan koran 'yan ta'adda

Sojojin Mali sun sanar da gano wani makeken kabari a Kidal da suka kwato kwanan nan daga hannun 'yan tawayen Abzinawa.  

Wani sojin Mali a yankin arewacin kasar
Wani sojin Mali a yankin arewacin kasar © REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Rundunar ta bayyana cewa, gano wannan kabari ya tabbatar da girman ta'asar da wadannan 'yan ta'adda suka aikata.    

Janyewar sojoji da 'yan sandan Majalisar Dinkin Duniya a yankin, ya kara dagula al’amura a arewacin kasar da ke fama da rikici, inda sabon rikici ya barke tsakanin sojojin Mali da kungiyoyin 'yan aware.  

'Yan awaren dai na zargi sojoji da kawayen su na Wagner da cin zarafin jama'a. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.