Isa ga babban shafi

'Yan sanda a Kenya na binciken kisan mutane da aka yi a wata gonar abarba

'Yan sandan Kenya sun ce, suna gudanar da bincike kan wasu mutane hudu da ake zargi da kashe mutane hudu a wata gonar abarba ta Del Monte da ke kusa da birnin Nairobi, watanni bayan wani rahoton da kafar yada labarai ta fitar ya ce jami'an tsaron da ke aiki a wurin sun kashe tare da kai farmaki ga mutanen kauyen.

Mazzauna kauyen sun ce, akwai gawawwakin da ake zargin an ci zarafinsu kafin a kashe su.
Mazzauna kauyen sun ce, akwai gawawwakin da ake zargin an ci zarafinsu kafin a kashe su. © Reuters
Talla

Abokai da ‘yan uwan wadanda abin ya shafa na baya-bayan nan sun bukaci gwamnati da ta shiga tsakani domin bayyana yadda mutanen hudu suka mutu a cikin wani kogi mai tazarar kilomita 40 daga Nairobi.

A farkon wannan shekarar ne wani bincike na hadin gwiwa da ofishin binciken aikin jarida na Biritaniya da jaridar Guardian suka gudanar ya gano wasu shaidun da suka ce jami'an tsaron da ke aiki da Del Monte sun kashe tare da cin zarafin mutanen kauyukan da ake zargi da kutsa kai cikin gonar abarbar.

Bayan kwanaki biyar ana bincike, an gano gawarwaki biyu a wani kogi a ranar Lahaddin da ta gabata, sai kuma karin wasu mutum biyu da aka gano a washe garin ranar, kamar yadda kafar yada labarai mai zaman kanta ta Citizen TV ta ruwaito.

Wani mazaunin kauyen mai suna, Peter Kamanzi, ya bayyana cewa an samu daya daga cikin gawawwakin da aka samu da raunuka a jikinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.