Isa ga babban shafi

'Yan awaren Kamaru sun hallaka mutum 9 a Arewacin kasar

'Yan awaren kasar Kamaru sun hallaka akalla mazauna kauyen Bamenyam guda 9 a wani kazamin harin da suka kai musu yau Talata, a yankin da yayi kaurin suna wajen tashin hankali. 

Nan wani hari ne da 'yan awaren suka gudanar a yankin Buea, da ke kudu maso yammacin babban birnin Kamaru, a watan Oktoba, 2018.
Nan wani hari ne da 'yan awaren suka gudanar a yankin Buea, da ke kudu maso yammacin babban birnin Kamaru, a watan Oktoba, 2018. AFP/File
Talla

Jami’in mulkin ‘yankin, David Dibango ya shaidawa gidan rediyo da talabijin na kasar cewar an kai harin ne a Bamenyam dake gundumar Bamboutous, kuma shi da kansa ya kidaya gawarwaki 9. 

Wani jami’in Jandarmeri a yankin ya tabbatarwa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP kisan gillar, Wanda ake zargin ‘yan awaren da aikatawa. 

Har yanzu babu wata sanarwar daukar alhakin wannan hari daga kungiyar 'yan awaren.

Hare-hare a yankin da ke amfani da harshen Faransaci na ci gaba da yin kamari, cikin shekaru biyu da suka gabata, yayin da 'yan tawayen ke ci gaba da hankoron kafa kasa mai cin gashin kanta.

Rikicin 'yan awaren ya kashe mutane sama da 6,000 tare da tilastawa kusan mutum miliyan guda baarin muhallansu, sakamakonkashe-kashen da suke fuskanta daga bangarorin da ke  rikici da juna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.