Isa ga babban shafi

An kashe wani dan jarida a yankin 'yan aware na kasar Kamaru

Rahotanni daga Kasar Kamaru na cewa, mayakan ‘Yan aware dauke da makamai sun harbe wani dan jarida da a Bamenda  hedikwatar yankin arewa maso yammacin kasar da ake anfani da turancin Ingilishi mai fama da rikici.

Dan jaridar Kamaru Anye Rhopann Nsoh (Anye Nde Nsoh) da wasu 'yan bindiga suka kashe a yankin 'yan aware. 07/05/23
Dan jaridar Kamaru Anye Rhopann Nsoh (Anye Nde Nsoh) da wasu 'yan bindiga suka kashe a yankin 'yan aware. 07/05/23 © Anye Rhopann Nsoh
Talla

Sanarwar kungiyar ‘yan jaridun kasar Kamaru na tabbatar da  kashe akalla ma’aikatan yada labarai uku cikin wannan shekara a kasar.

Dan Jarida

An kashe Anye Nde Nsoh, babban jami’in ofishin jaridar the Advocate na yankin yamma da arewa maso yamma, ne a wata mashaya dake unguwar Ntarikon da ke garin Bamenda, lokacin da wasu da ba a san ko su waye ba suka bude masa wuta, kamar yadda abokin aikinsa Melanie Ndefru, wadda ke kusa da wurin da harin ya faru ta tabbatar.

A farkon wannan shekara, an kashe wani dan jarida mai gabatar da shirin rediyo a wani hari da aka kai masa a Yaounde babban birnin kasar, lamarin da ya sa Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa game da yanayin kafafen yada labarai.

Kungiyar ‘yan jarida masu magana da Ingilishi ta Kamaru (CAMASEJ) ta tabbatar da mutuwar Nsoh tare da yin kira da a gudanar da bincike.

Yankin 'Yan aware

Mutuwar Nsoh ta zo ne a daidai lokacin da ake gwabza fada tsakanin hukumomin Kamaru da wasu kungiyoyin ‘yan aware a yankunan masu amfani da turancin Ingilishi, wanda ya rikide zuwa tashin hankali a shekarar 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.