Isa ga babban shafi

An saki mata sama da 30 da 'Yan aware suka yi gurkuwa da su a Kamaru

Rahotanni daga kasar Kamaru na cewa an sako matan nan tsoffi sama da 30 da 'yan aware suka yi garkuwa da su a yankin da ake amfani da turancin Ingilishi na kasar mako guda bayan zanga-zangar adawa da harajin da suka yi.

Wasu jami'an 'yan sandan Kamaru dake sintiri a Yaounde babban birnin kasar.
Wasu jami'an 'yan sandan Kamaru dake sintiri a Yaounde babban birnin kasar. AP - Sunday Alamba
Talla

 

Da yake tabbatar da hakan, Denis Omgba Bomba, shugaban hukumar kula da harkokin yada labarai a ma’aikatar sadarwa ta kasa ya ce an sako matan ne kwanaki uku bayan da aka sace su a yankin Arewa maso Yammacin kasar, batare da karin bayanin kan yanayin sakin ba, ko batun biyan kudin fansa. Sai dai yace an azabtar da matan sosai.

‘Yan ta’adda dauke da muggan makamai ne suka yi garkuwa da matan a kauyen Kedjom Keku kwana guda bayan gudanar da zanga-zangar adawa da harajin wata-wata da ‘yan awaren suka kakabawa gidaje.

Wani magajin gari a yankin ya tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa an sako mutanen, inda ya bukaci a sakaya sunansu.

Omgba Bomba ya ce baya son yin karin bayani kan sakin matan ko kuma halin da suke ciki, sai dai ya bayyana cewa daya ta samu karyewar kafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.