Isa ga babban shafi

'Yan awaren Kamaru sun yi gargadi kan jana'izar Frundi a yankinsu

Shugabannin ‘Yan aware masu fafutukar kafa jamhuriyar Ambazonia a kasar Kamaru, sun yi gargadi kan jana’izar tsohon jagoran jam’iyyun adawa a kasar Ni John Frundi a yankin su.

John Fru Ndi daga yankin yan aware na kasar Kamaru
John Fru Ndi daga yankin yan aware na kasar Kamaru rfi hausa
Talla

Cikin wata sanarwa da ya fitar kuma wasu jaridun kasar Kamaru suka wallafa, shugaban daya daga cikin kungiyoyin ‘yan awaren Cho Ayaba dake zaune a kasar Norway, marigayin Frundi tsohon shugaban jam’iyyar SDF mai adawa bai cancaci a yi masa jana’iza a Bamenda ba saboda da abin da ya kira kasancewarsa mayaudari wanda ya ci amanar yankin nasu da ake magana da harshen Ingilishi.

Don haka Ayaba Cho ya ce ba za su taba amincewa a kawo gawar marigayin zuwa yankinsu ba, kuma duk wanda ya yi yunkurin haka ya yi kuka da kansa.

Shugaban 'Yan awaren yace, Frundi bai taba taimakawa fafutukar su ta neman warewa daga Kamaru don kafa Ambazonia ba, hasali ma ya hada kai da gwamnatin Paul Biyu domin cutar da masu gwagwarmaya da makamai.

Tuni ya sanar da sanya dokar hana fita na kwanaki biyu wato 28 da 29 ga wannan wata na Yuli a kauyen Mezam. Domin kawo cikas ga shirin dawo da gawar Ni John Frundi gida domin yi masa jana’izan ban girma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.