Isa ga babban shafi

Sarkin Ingila Charles na uku na ziyara a kasar Kenya

Sarkin Ingila Charles na uku, ya fara ziyarar kwanaki hudu a kasar Kenya wannan Talata, ta farko a wata kasa da Ingila ta rena tun lokacin da ya dare kan karagar mulki, daidai lokacin da ya ke fuskantar kiraye-kirayen cewa lalle sai ya nemi gafarar 'yan kasar Kenya kan cin zarafin da aka yi lokacin da Birtaniya ta yi ma ta mulkin mallaka.

Sarkin Ingila Charles na Uku na ziyara a kasar Kenya,31/10/23
Sarkin Ingila Charles na Uku na ziyara a kasar Kenya,31/10/23 REUTERS - THOMAS MUKOYA
Talla

Sarki Charles na uku tare da rakiyar mai dakinsa Sarauniya Camilla, sun samu kyakkyawar tarba daga shugaban kasar Kenya William Ruto da mukarrabansa a Nairobi babban birnin kasar da safiyar wannan Talata, tare da faratin soji na ban girma.

Fadar Buckingham ta ce ziyarar ta nuna yadda kasashen biyu ke hadin gwiwa sosai a fannin bunkasa tattalin arziki, sauyin yanayi da kuma batutuwan tsaro.

Sarkin Ingila Charles na Uku na ziyara a kasar Kenya,31/10/23
Sarkin Ingila Charles na Uku na ziyara a kasar Kenya,31/10/23 AFP - SIMON MAINA

Charles zai gana da ’yan kasuwa da masu fasahar kere-kere na Kenya sannan ya ziyarci wuraren yawon shakatawa da kallon namun daji. Shi da Camilla kuma za su yi tattaki zuwa birnin Mombassa mai tashar jiragen ruwa na kudu maso gabashin kasar.

Mulkin Mallaka

Yawancin 'yan Kenya, sun fi mayar da hankali kan abin da Charles zai ce game da cin zarafi a zamanin mulkin mallaka, da suka hada da azabtarwa, kashe-kashe da kuma kwace filaye da yawa, wadanda har yanzu yawancinsu na turawan Burtaniya ne da kamfanonin waje.

Kimanin mutane 10,000 ne aka kashe musamman daga kabilar Kikuyu a lokacin da ake kokarin murkushe su.

Bukin 'Yancin Kai

Ziyarar masarautar ta zo ne a daidai lokacin da Kenya ke shirin bikin cika shekaru 60 da samun 'yancin kai daga Birtaniya.

Sarkin Ingila Charles na Uku na ziyara a kasar Kenya,31/10/23
Sarkin Ingila Charles na Uku na ziyara a kasar Kenya,31/10/23 AP - Brian Inganga

A shekarar 1952 ne mahaifiyar Charles, marigayiya Sarauniya Elizabeth ta biyu ta sami labarin rasuwar mahaifinta, Sarki George na shida, lokacin tana ziyara a kasar Kenya, wanda ke nuna farkon mulkinta na shekaru 70 mai cike da tarihi.

Ko da yake gwamnatin Kenya ta ce za a tattauna batutuwan da suka shafi muhalli, fasaha, kirkire-kirkire da karfafawa mata, amma bukatar neman afuwar ta mamaye batun ziyarar sarkin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.