Isa ga babban shafi

Al'ummar Kipsigis da Talai a Kenya za su maka Birtaniya a kotun Turai kan filaye

Wasu ‘yan kasar Kenya sun sha alwashin shigar da karar Birtaniya a gaban kotun Turai, saboda kwace musu filayensu a lokacin mulkin mallaka.

Wani yanki mallakin al'ummar ta Kipsigis da Talai da Birtaniya ta kwace tun shekarun 1930.
Wani yanki mallakin al'ummar ta Kipsigis da Talai da Birtaniya ta kwace tun shekarun 1930. AFP
Talla

Lauyoyin wadanda aka kora daga yankin Rift Valley na kasar Kenya suka ce watsi da gwamnatin Birtaniya ta yi da korafe-korafen wadanda abin ya shafa sun saba ka’idar yarjejeniyar kare hakkin bil'adama ta Turai da kasar ta rattaba wa hannu.

Mista Joel Kimutai Bosek, wanda ke wakiltar al'ummar Kipsigis da Talai ya ce "Gwamnatin Burtaniya ta kauce wa duk wata hanya ta duba bukatun, don haka ba su da zabin da ya wuce mika batun gaban kotu don biyan bukatun wadanda ya ke karewa.

A farkon karni na 20 turuwan mulkin mallakar Birtaniya suka kori al’ummar Kipsigis da Talai daga yankinsu na asali na kaka da kakanni da ke kewayen Kericho, dake har ya zuwa yanzu ke zama cibiyar gonakin shayi, wanda manyan kamfanonin shayi na ƙasa da ƙasa irinsu Unilever, Finlay's da Lipton ke noma a can.

A shararar 2019, kimanin Wadanda abin ya shafa -- sama da dubu 100 suka rattaba hannu kan wani korafin da suka shigar gaban Majalisar Dinkin Duniya, inda wani kwamitin Majalisar ya nuna damuwa kan gazawar Birtaniya na bada hakuri ko makamaicinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.