Isa ga babban shafi

Kenya ta hana taron manema labarai saboda abin da Birtaniya ta yi

‘Yan sandan Kenya sun hana gudanar da wani taron manema labarai, da aka shirya domin sake fallasa zargin cin zarafin bil’adama da ake wa sojojin Birtaniya a kasar, sa’o’i kadan kafin Sarki Charles ya isa kasar domin ziyarar aiki ta kwanaki hudu.

Wata Mata 'yar kasar Kenya da ke kallon hotunan Sarki Charles.
Wata Mata 'yar kasar Kenya da ke kallon hotunan Sarki Charles. © REUTERS/Thomas Mukoya/File photo Acquire Licensing Rights
Talla

Fadar Buckingham ta ce ziyarar Sarki Charles za ta yi waiwaye kan wasu batutuwa da suka faru tsakanin Birtaniya da Kenya, wacce ta yiwa mulkin mallaka na fiye da shekaru sittin, kafin kasar da ke gabashin Afirka ta samu ‘yancin kai a shekarar 1963.

Zarge-zargen da ake magana a kai, sun faru ne bayan kawo karshen mulkin mallakar da Birtaniya ta yi wa Kenya, inda mazauna Lolldaiga da ke tsakiyar kasar ta Kenya, suka zargi sojojin Birtaniya da ke wani sansanin horowa kusa da su da haddasa gobarar daji a shekarar 2021 da ta lalata da dama daga cikin gandun dajin da ke yankin, tare raunata al’ummar yankin, sai kuma zargin  kisan wata mata da sojojin Birtaniya suka yi a shekarar 2012.

Hukumomin Birtaniya a baya sun yi alkawalin gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa sojojin da ke sansani.

Toh sai dai kafin gudanar da taron manema labaran a wani otal da ke birnin Nairobi a Litinin din nan, wata babbar mota dauke da jami’an ‘yan sanda akalla 20 da kuma wasu a kananan motoci biyu suma dauke da 'yan sanda, sun tare hanyar shiga wajen da aka shirya gudanar da taron, kamar yadda wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya bayyana.

Rundunar ‘yan sandan kasar ta kuma gargadi mahukunta Otel din da  kada su bari a gudanar da taron, in ji James Mwangi, shugaban kungiyar kare hakkin bil’adama da ke tallafa wa wadanda aka ci zarafinsu a Lolldaiga.

Kakakin rundunar 'yan sandan Kenya ta ki cewa kan batun, a lokacin da Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya tuntube ta, haka nan ofishin jakadancin Brrtaniya da ke Nairobi bai ce komai kan lamarin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.