Isa ga babban shafi

Alfanun ziyarar Shugaban Gwamnatin Jamus Olaf Scholz a Najeriya da Ghana

Shugabar gwamnatin Jamus na ziyara a Afirka, daga wannan Lahadi 29 ga watan Oktoba, a karo na uku tun bayan hawansa mulki shekaru biyu da suka gabata. Olaf Scholz zai ziyarci Najeriya da Ghana. Shugaban Tarayyar Jamus Frank-Walter Steinmeier zai ziyarci Tanzania da Zambia daga ranar Litinin 30 ga watan Oktoba. tafiye-tafiye guda biyu da ke nuna karuwar sha'awar Jamus a Afirka.

Shugaban Gwamnatin Jamus
Shugaban Gwamnatin Jamus AP - Markus Schreiber
Talla

Tattalin Arziki, tsaro da diflomasiya za su kasance a cikin jerin abubuwan tafiyar Olaf Scholz zuwa Najeriya da Ghana. Kasashen biyu za su mayar da hankali a daya geffen bangaren makamashin, a wannan lokaci da Jamus ke bukatar shi tun bayan  kawo karshen isar da iskar gas da Rasha ta yi zuwa wasu kasashen na Turai.

Hakan na tilastawa Jamus kara hulda da sauran kasashe. Jamus na daga cikin kasashen da ke neman kula huldar tattalin arziki da Najeriya.

Shugaban Gwamnatin Jamus  Olaf Scholz.
Shugaban Gwamnatin Jamus Olaf Scholz. AP - Fabian Sommer

 

Olaf Scholz zai ziyarci wata cibiyar kula da yan cin rani  a karkashin hulda tsakanin  Jamus da Najeriya. Wannan ya shafi, a gefe guda, maido da masu neman mafaka da aka ƙi, amma kuma don buɗe damar yin maraba da ƙwararrun ma'aikatan da Jamus ke buƙata. Kyakkyawan horon da kwararrun  na Ghana ke amfana da shi na daga cikin tsarin da Jamus ke alfahari da shi..

 

Shugaban Najeriya Tinubu
Shugaban Najeriya Tinubu © Reuters

 

A ƙarshe, manufofin yanki na kan ajandar wannan tafiya. Olaf Scholz zai gana ne, baya ga shugabannin kasashen biyu, shugaban hukumar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS. Ziyarar dai na zuwa ne makonni uku kafin gudanar da taron zuba jari na G20 na Afirka karo na hudu, wanda za a yi a babban birnin Jamus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.