Isa ga babban shafi

Jamus ta mayarwa Najeriya kayakin tarihin da Birtaniya ta sace a karni na 16

Jamus ta mayarwa Najeriya kayakin tarihi fiye da 20 wadanda turawan mulkin mallakar Birtaniya suka kwashe fiye da shekaru 100 da suka gabata.

Wasu daga cikin kayakin tarihin da Jamus ta mikawa Najeriya.
Wasu daga cikin kayakin tarihin da Jamus ta mikawa Najeriya. AP - Wolfgang Kumm
Talla

A jiya talata ne Jamus ta mika kayakin tarihin fiye da 20 wadanda sojojin turawan mulkin mallaka daga Birtaniya suka wawushe tun a karni na 16 da 18 a wani yunkuri na maidawa Afrika kayakin tarihinta da turawa suka wawushe.

Tarin kayakin tarihi masu matukar muhimmanci ne Turawan mulkin mallakar daga kasashen Birtaniya Faransa da kuma Belgium suka sace daga Afrika tare da sayar da su ga gidajen tarihin Amurka da sauran kasashen Turai.

Matakin Amurkan na mayar da kayakin tarihin na zuwa a dai dai lokacin da kiraye-kiraye ke kara tsananta game da bukatar mayarwa nahiyar Afrika kayakin tarihinta da Turawa suka sace daruruwan shekaru da suka gabata.

Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock da kanta ta yi tattaki zuwa Abuja fadar gwamnatin Najeriya tare da mika kayakin tarihin.

A jawabinta wajen mika kayakin tarihin, ministar ta ce kayakin da ta ke mikawa wani bangare ne na tarihin Najeriya, tarihin su waye ‘yan Najeriya domin gyara kuskuren da aka tafka daruruwan shekaru da suka gabata.

Bayanai sun nuna cewa Turawan Birtaniya sun kwashe tarin kayan tarihi da suka kunshi muhimman gumaka lokacin da sojojinsu suka farmaki masarautun gargajiya da dama ciki har da birnin Benin inda suka samu tarihin dadaddun kayakin tarihi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.