Isa ga babban shafi

Jamus za ta mikawa Najeriya wasu kayayyakin tarihi da ta kwashe a karni na 19

Kasar Jamus za ta mayarwa Najeriya kayayyakin tarihi da aka kera da tagulla, wadanda kuma aka kwashe a Benin cikin karni na 19.

Sojojin Burtaniya sun kwashe daruruwan mutum-mutumi da aka kera da tagulla tun daga karni na 13
Sojojin Burtaniya sun kwashe daruruwan mutum-mutumi da aka kera da tagulla tun daga karni na 13 © 网络图片
Talla

An dai rattaba hannun ne tsakanin cibiyar Al'adun Prussian da Hukumar Kula da Gidajen Tarihi ta Najeriya don canja wurin mallakarsu daga tarin kayan tarihi na Ethnological da ke Berlin zuwa Najeriya.

Kwamishiniyar al'adu ta Jamus Claudia Roth ta ce wannan misali ne ga gidajen tarihi a Jamus da ke da tarin kayan tarihi a zamanin mulkin mallaka kuma za a ci gaba da cimma yarjejeniya nan da watanni masu zuwa.

Sojojin Burtaniya sun kwashe daruruwan mutum-mutumi da aka kera da tagulla tun daga karni na 13 a lokacin da suka mamaye daular Benin da ke yankin kudu maso yammacin Najeriya a shekara ta 1897.

Wadannan kayayyakin kayan tarihi an ajiye su ne a gidajen tarihi da ke kasashen Turai da Amurka kuma kasashen Afirka sun kwashe shekaru suna fafutuka don kwato su.

A watan Yuli ne Jamus ta mayar wa Najeriya kashin farko na kayayyakin tarihin, inda ake dakon sauran kayayyakin a cikin wannan shekara.

Sai dai bisa bayanai, kusan kashi uku na kayayyakin za su ci gaba da zaman lamuni a Jamus tsawon shekaru 10 kuma za a baje kolin su a dandalin Humboldt a Berlin.

Masana tarihin fasaha na Faransa sun yi kiyasin cewa kusan kashi 90 cikin 100 na kayayyakin tarihi na Afirka an yi imanin cewa suna cikin Turai.

Kasashen Afirka na ci gaba da fafutuka neman dawo da kayayyakinsu na tarihi da masu bincike da ‘yan mulkin mallaka suka wawashe yayin da cibiyoyin adana kayan tarihi na kasashen Yamma ke kokawa da al’adun mulkin mallaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.