Isa ga babban shafi

Kamfanin Siemens ya kammala gwajin manyan na’urorin samar da wutar Najeriya

Katafaren kamfanin samar da wutar lantarkin kasar Jamus da ake kira Siemens ya kammala gwajin manyan na’urorin raba wutar da ake kira transforma da gwamnatin Najeriya ta sayo domin bunkasa harkar bada wutar a cikin kasar.

Kamfanin Siemens ya kammala gwajin manyan na’urorin samar da wutar Najeriya, 30/07/22
Kamfanin Siemens ya kammala gwajin manyan na’urorin samar da wutar Najeriya, 30/07/22 © Nigerian Ministry of Power
Talla

Shugaban kamfanin lantarkin Najeriya Kenny Anuwe ya jagoranci tawagar gwamnatin kasar zuwa kamfanin Siemens dake Trento a Italia inda aka gudanar da gwajin na’urorin a gaban su domin tabbatar da ingancin su.

Shirin gwamnati

An dai sayo wadannan manyan na’urorin transforma ne a karkashin shirin gwamnati mai ci na inganta harkar samar da wutar da ake kira ‘Presidential Power Initiative‘, wanda shine tsarin da zai kunshi matakai daban daban na samar da kayan aiki da kuma inganta hanyar rarraba wutar zuwa sassan Najeriya ta hanyar amfani da sabbin na’urorin zamani.

Ministan kula da wutar lantarki Injiniya Abubakar D. Aliyu yace gwamnatin shugaba Muhammadu buhari ta dukufa wajen ganin an shawo kan matsalar samar da wutar lantarki ta hanyar aiwatar da wannan kwangilar na Siemens, kuma matakin farko na aikin shine shigar da wadannan manya manyan na’urorin transforma guda 10 da kuma tashoshin samar da wutar na tafi da gidanka guda 10.

Matslolin lantarki

Injiniya Aliyu ya yi karin haske dangane da tsarin samar da wutar lantarkin na kasa, inda yace ba’a taba samun lokacin da ya rushe gaba daya ba, duk da yake akan samu matsala lokaci zuwa lokaci, kuma akan gyara.

Ministan yace kuskure ne yadda ake cewa harkar samar da wutar ya ruguje gaba daya, lura da cewar tun lokacin da ya kama aiki an mayar ad hankali ne wajen inganta hanyoyin samar da wutar da kuma takaita matsalolin da ake samu na katsewar ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.