Isa ga babban shafi
DR Congo

Joseph Kabila ya sanar da dage zabe zuwa shekarar 2018

Shugaban Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo, Joseph Kabila ya sanar da dage zaben kasar zuwa watan Disamba na shekarar 2018, acewarsa hakan zai baiwa hukumar zaben damar kammala shirye shiryen da suka kamata.

Shugaban Jamhurriyar Demokradiyar Kongo Joseph Kabila ya sanar da dage zaben kasar zuwa 2018
Shugaban Jamhurriyar Demokradiyar Kongo Joseph Kabila ya sanar da dage zaben kasar zuwa 2018 DR
Talla

Shugaban yace an dauki matakin ne dan ganin ba a hana wasu mutane kusan miliyan 10 damar shiga zaben ba saboda basu da rajista.

Dama dai a karshen wannan shekarar ne wa’adin Kabila na biyu ke karewa, amma yace zai tsaya wa’adin na uku abinda ‘yan adawa suka ce ba zata sabu ba.

Sakamakon yunkurin ci gaba da mulki da shugaba Kabila ya yi a bayan ya haifar da  rikici da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da jefa al’umma cikin zaman dardar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.