Isa ga babban shafi
Dr Congo

Jagoran 'yan tawayen Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo ya ki halartar kotu

Tsoho jagoran ‘yan tawayen Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo Bosco Ntanganda, ya sake kin halartar shari’ar da ake yi masa a kotun hukunta manyan laifukkan yaki ICC.

Sakataren kungiyar kare hakkin dan'adam ta CENCO da ke Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo l'Abbé Léonard Santedi,
Sakataren kungiyar kare hakkin dan'adam ta CENCO da ke Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo l'Abbé Léonard Santedi, cenco.cd
Talla

Ntanganda yanzu ya shafe rana ta 7 da yake yajin cin abinci.

Ntaganda yana nuna rashin jin dadi kan irin mu’amalar da aka yi masa a lokacin da yake tsare, inda ya ce a shirye yake ya mutu, bayan ya zargi kotun ICC kan rashin bashi damar kare kan sa.

Ntaganda, wanda aka tsare dashi a sansanin wadanda ake tuhuma na kotun ta ICC tun bayan da ya mika wuya a shekarar 2013, ya kuma umurci lauyansa da ya daina kareshi.

Ntaganda wanda ake yi wa lakabi da Terminator, ya musanta zage zarge 18 da ake yi masa na aikata kisan jama’a karkashin kungiyarsa ta FPLC a kasar ta Congo.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.