Isa ga babban shafi
DRC

Katolika ta bukaci a mutunta shirin zabe a DRC

Shugabannin mabiya darikar katolika a Jamhuriyar Demokiradiyar Congo sun bukaci gudanar da zaben shugaban kasar kamar yadda aka shirya da kuma saukar shugaba Joseph Kabila daga karagar mulki.

Joseph Kabila tare da wasu limaman addinin Kirista a Jamhuriyar Demokradiyar Congo
Joseph Kabila tare da wasu limaman addinin Kirista a Jamhuriyar Demokradiyar Congo ©RFI/Sonia Rolley
Talla

Shugabanin mabiya darikar sun ce, ya zama wajibi su mutunta kundin tsarin mulkin kasar wanda ya tanadi wa’adi biyu ga kowanne shugaban kasa.

Shugaban taron mabiyan Leonard Santedi ya ce, kauda kundin tsarin mulkin na iya jefa kasar cikin tashin hankalin da basa son gani, inda ya zargi 'yan siyasar kasar da yunkurin yin haka.

Shugabanin sun kuma koka kan tabarbarewar tsaro da kare hakkin bil Adama a kasar musamman a gabashin kasar inda ake ci gaba da kashe mutane.

Shi dai shugaba Joseph Kabila na neman sake takarar wa’adi na uku ne, abinda 'yan kasar ke adawa da shi.

Ana saran wa’adinsa zai kare a ranar 19 ga watan disamba mai zuwa, bayan hawansa karagar mulki a shekarar 2001.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.