Isa ga babban shafi
Congo Kinshasa

Magoya Bayan Shugaba Kabila Na Neman Ya Zarce

Dubban magoya bayan shugaban kasar Congo Kinshasa suka shiga wani gangami da aka gudanar Asabar  a birnin Kinshasa domin taya shugaban kasar Joseph Kabila bukin dake cika shekaru 45 da haihuwa.

Shugaban Congo Joseph Kabila
Shugaban Congo Joseph Kabila AFP PHOTO / GWENN DUBOURTHOUMIEU
Talla

Mahalarta wannan buki sunyi amfani da wannan dama domin yin kira ga shugaban kasar da ya aiwatar da zaben raba gardama domin ganin ya sami amincewar ‘yan kasar don ya zarce da mulki.

Wannan zuga shugaban da akayi bisa dukkan alamu zai kara harzuka ‘yan adawa da Gwamnatin wannan shugaba daya dare madafun iko tun shekara ta 2001, bayan an kashe mahaifinsa shugaban wancan lokaci.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.