Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Congo

Kungiyoyi 180 sun bukaci karfafa dakarun MDD saboda zaben DR Congo

Kimanin kungiyoyin fararar Hula da masu fafutukar kare hakkin dan’Adam 180 ne, suka bukaci karawa dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, karfi a kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, domin ganin, an yi zaben kasar cikin kwanciyar hankali a watan Nuwamba mai zuwa

Dakarun Majalisar Dinkin Duniya
Dakarun Majalisar Dinkin Duniya resolutionpossible.co.uk
Talla

Bukatar kungiyoyin na zuwa ne, a daidai lokacin da dakarun Majalisar Dinkin Duniyan ke shirin kawo karshen ayyukan su a kasar.

A cewar Kungiyoyyin, lura da rikicin siyasar kasar ,samun goyon bayan Majalisar nada Muhimmaci, domin tabbatar da kare rayukan alumma a kasar.

kungiyoyin sun bada misalin mutuwar mutane 42 a taron gangamin adawa da yunkurin shugaba kabila na neman wa’adi na uku a karagar mulki, kuma sun ce, wannan ya isa a gamsu da manufarsu ta bukatan taimakon Majalisar Dinkin Duniya.

A shekarra ta 2013, Dubban mutane suka rasa rayukansu baya ga sama da dubu 100 da suka tsere daga gidajensu sakamakon wani rikici daya barke tsakanin yan’tawaye da Dakarun Soji a gabshin kasar kamar yadda Majaliasar Dinkin Duniya ta tabbatar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.