Jam’iyyar adawa ta janye daga tattaunawa da Kabila
Babbar Jam’iyyar adawar kasar Jamhuriyar Demokiradiyar Congo ta sanar da ficewa daga tattaunawar da ta ke da wakilan shugaban kasar Joseph Kabila kan shirin zaben shugaban kasar da za a yi a shekara mai zuwa.
Wallafawa ranar:
Wakilan bangarorin biyu na ganawa ne a Turai don tattauna yadda za a gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali a watan Nuwamba na shekarar 2016.
Ma su sa ido na zargin shugaba Joseph Kabila da yunkurin tsawaita mulkinsa idan wa’adinsa na biyu ya kawo karshe shekara mai zuwa.
Wakilan Jam’iyyar UDPS ta madugun adawa Etienne Tshisekedi na tattaunawa da wakilan gwamnatin Kabila ne a Brussels, kuma a ranar Lahadi ne bangaren jam’iyyar adawar ta fitar da sanarwar ficewa daga zauren tattaunawar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu