Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Congo

An rantsar da Kabila, amma Congo ta rabu biyu

Shugaban Kasar Jamhuriyar Demokradiyar Congo, Joseph Kabila, ya yi alkawarin hadin kan kasar, da kare muradunta, lokacin da ya ke karbar rantsuwar wa’adi na biyu, bayan zaben shi da ya samu suka daga sassan duniya da dama. 

Lokacin da Joseph Kabila. ke gabatar da Jawabi a gaban magoya bayansa, da wasu shugabannin kasashen Afrika da suka hada da  Robert Mugabe,
Lokacin da Joseph Kabila. ke gabatar da Jawabi a gaban magoya bayansa, da wasu shugabannin kasashen Afrika da suka hada da Robert Mugabe, AFP/GWENN DUBOURTHOUMIEU
Talla

Sakamakon zaben Kabila ya fuskanci Suka daga kasashen duniya da madugun adawa babban mai hamayya da shugaban Etienne Tshisekedi wanda ya shaidawa ‘yan kasar shi ne halattacen shugaban kasa.

Kasar Amurka da kasashen Turai sun soki kotun kolin kasar bisa amincewa da sakamakon zaben bayan ta amsa samun kura-kurai a zaben.

Mista Kabila, bayan karbar rantsuwar aiki a gaban magoya bayansa ya sha alwashin hada kan kasa tare da kare hakkokan al’ummar kasar.

Sai dai babban mai adawa Tshisekedi, yace zai gudanar da wata kazamar zanga-zanga tare da kira ga jami’an tsaron kasar domin amincewa da shi a matsayin sabon shugaban kasa.

Tshisekedi ya taba rike mukamin Fira Ministan kasar, karkashin shugabancin Mobutu Sese Seko.

Yanzu haka dai ana zaman dar-dar a cikin kasar inda hankulan ‘yan kasar ya rabu gida biyu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.