Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Congo

Za’a rantsar da Kabila, amma Tshisekedi yace shi ne Shugaban Congo

A yau Talata an girke jami’an tsaro a Kinsasha babban birnin kasar Jamhuriyyar Demokradiyya Congo kafin rantsar da shugaba Joseph Kabila, a dai dai lokacin da abokin hamayyarsa Etienne Tshisekedi ke jaddada karbar rantsuwar shugabancin kasar.

'Yan sandan kasar Jamhuriyyar Congo sun yi damara dauke da garkuwa a birnin Kinsasha babban birnin kasar
'Yan sandan kasar Jamhuriyyar Congo sun yi damara dauke da garkuwa a birnin Kinsasha babban birnin kasar Daniel Finnan
Talla

Rehotanni daga Kinsasha na cewa ‘Yan sanda dauke da tankunan yaki sun kewaye birnin tare da tarwatsa magoya bayan Etienne Tshisekedi.

A ranar Lahadi Etienne Tshisekedi ya yi ikirarin kansa matsayin zababben shugaban kasa duk da kotun kolin kasar da hukumar zabe sun ce Joseph Kabila ne ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 28 ga watan Nuwamba.

Sai dai wakilan kasashen duniya da suka sa ido a zaben sun yi zargin samun kura-kurai da tabka magudi a zaben.

Kabila wanda tun a shekarar 2006 ne yake shugabancin kasar, a yau Talata ne za’a rantsar da shi, sai dai abokin hamayyar shi Etienne Tshisekedi yace a ranar lahadi za’a rantsar da shi matsayin sabon shugaban kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.