Isa ga babban shafi
Janhuriyar Demokaradiyar Congo

Kotun Kolin kasar Congo Kinshasa ta amince da sakamakon zaben Shugaban kasa

Kotun kolin kasar Janhuriyar Demokaradiyar Congo ta amince da sakamakon zaben Shugaban kasa, wanda ya baiwa Shugaba Joseph Kabila nasarar wani wa’adin shekaru biyar.

Joseph Kabila shugaban kasar Janhuriyar Demokaradiyar Congo
Joseph Kabila shugaban kasar Janhuriyar Demokaradiyar Congo AFP/Gwenn Duborthomieu
Talla

Kotun ta yi watsi da bukatar neman soke zaben na ranar 28 ga watan jiya na Nowamba, da ‘yan adawa suka nema, saboda yadda rudani da rashin bin ka'ida suka dabaibaye zaben.

Shugaba Kabila na Jnahuriyar Demokaradiyar Congo, dan shekaru 40 da haihuwa, ya kada babban mai kalubalantarsa kuma dadadden madugun ‘yan adawa Etienne Tshisekedi mai shekaru 78 da haihuwa.

Shugaban ya dauki madafun iko a shekara ta 2001, yana da shekaru 30, bayan kisan da aka yi wa mahaifinsa Marigayi Shugaba Laurent Kabila.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.