An sake samun tsaikun sakamakon zabe a Jamhuriyyar Congo
Hukumar zaben kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta sake dage bayar da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar, har zuwa yau juma’a.
Wallafawa ranar:
A ranar 28 ga watan Nuwamba ne aka gudanar da zaben shugaban kasar, da farko an shirya bayar da sakamakon zaben a ranar talata daga bisani kuma aka dage zuwa jiya Alhamis, yanzu kuma hukumar zaben tace sai a yau Juma’a ne za’a samu sakamakon bayan ta kammala diba sahihancin sakamakon..
Kafin bayyana sakamakon, sai kotun kolin kasar ta yi nazari akai, tare kuma bayyana wanda ya lashe a ranar 17 ga wannan watan.
Wannan matakin ya sake cusa shakku da tsoron sake samun aukuwar tashin hankuli a cikin kasar inda ake zaman dar-dar tsakanin magoya bayan ‘Yan adawa da gwamnatin kasar.
Sakamakon farko da aka fitar ya nuna shugaba Joseph Kabila ne ke jagoranci da yawan kuri’u kashi 48.9, sai kuma abokin hamayyarsa Etienne Tshisekedi day a samu yawan kuri’u 33.3.
‘Yan adawa a kasar sun yi na’am da tsaikun da aka samu na bayyana sakamakon zaben, domin suna ganin hukumar zaben tana kokarin kamanta adalci ne a zaben, amma Jam’iyyar Madugun adawa Etienne Tshisekedi ta yi barazar kalubalantar zaben idan har aka bayyana shugaba Kabila ne ya lashe zaben.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu