Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Congo

Mutane 3,000 sun kauracewa Kinshasha domin gudun rikici a Congo

Kungiyar Kasashen Afrika ta AU, ta bukaci ‘Yan siyasar kasar Jamhuriyar Demokradiyar Congo, yin taka tsan-tsan, bayan 'Yan adawar kasar sun bayyana rashin amincewarsu da wani kashi na sakamakon zaben kasar da aka fitar, wanda ya nuna shugaba Joseph Kabila na kan gaba.

Magoya bayan madugun adawa Etienen Tshisekedi bayan barkewar rikici kafin gudanar da zaben shugaban kasa a Congo
Magoya bayan madugun adawa Etienen Tshisekedi bayan barkewar rikici kafin gudanar da zaben shugaban kasa a Congo REUTERS / Finbarr O'Reilly
Talla

Shugaban gudanarwar kungiyar, Jean Ping, yace rashin kai zuciya nesa, na iya haifar da tashin hankali a kasar.

Sakamakon ya nuna shugaba Kabila ya samu kuri’u sama da miliyan uku, da dubu dari biyu, yayin da madugun adawa Etienne Tshisekedi ya samu sama da miliyan biyu, da dubu dari biyu, daga kashi talatin da uku na kuri’un da aka kirga.

Akalla ‘Yan kasar Jamhuriyar demokradiyar Congo 3,000 suka tsere daga birnin Kinshasa zuwa Congo Brazaville, don kaucewa tashin hankalin zabe.

Wani jami’in shigi da fice na kasar Congo, ya shaidawa Ministan cikin gidan kasar, cewar mutane da suka tsallaka zuwa kasar ranakun asabar da lahadi, sun zarce 3,000.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.