Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Congo

‘Yan adawa Sun nemi soke zaben Shugaban kasa a Congo

Hudu daga cikin manyan masu kalubalantar Joseph Kaliba Shugaban kasar Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo, a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Litinin, sun nemi soke sakamakon zaben, saboda tashin hankali da magudi da aka tabka a zaben.

Akwatin zaben shugaban kasa a da aka gudanar a kasar Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo
Akwatin zaben shugaban kasa a da aka gudanar a kasar Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo Daniel Finnan
Talla

Vital Kamerhe tsoho Minista a gwamnatin, yace an yi dangwale ga kuri’u, domin Kabila ya samu nasara, tare da hana wasu masu kada kuri’a zabe.

Sauran ‘Yan takarar sun nemi al’ummar kasar su yi watsi da sakamakon zaben. Bayan samun mutuwar Akalla mutane takwas a rikicin daya biyo bayan zaben kasar.

‘Yan Takarar shugabancin kasar hudu Kengo wa Dondo da Antipas Mbusa Nyamwisi da Adam Bombole sun ce sakamakon zaben abun kyamata ne.

Sai dai Madugun adawa Tshisekedi ya nisanta kan shi da kiran soke zaben na ‘Yan adawa bisa tunanin Jam’iyyarsa ta UDPS zata lashe zaben.

A cewar Tshisekedi matakan da Mista Kabila ya bi na magudi basu yi aiki ba don baya goyon bayan soke zaben har sai an bayyana sakamakon zaben.

Kabila mai shekaru 40 na haihuwa ana has ashen shi zai lashe zaben tsakanin shi da ‘Yan takara 10. Kuma kimanin ‘Yan takara 18,500 ne neman kujarun Majalisar kasar 500.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.