Isa ga babban shafi
Janhuriyar Demokaradiyar Congo

Tashin hankali ya barke cikin wasu mazabun Congo Kinshasa

Hukumomin kasar Janhuriyar Demokaradiyar Congo sun sanar da cewa mutane dauke da bindigogi sun aike da mutane 3 lahira yau Litini, a wata tashar da ake jefa kuriu, a zaben Shugaban kasar da 'yan majalisu aka yi.

Daniel Finnan
Talla

Bayanai na nuna cewa lamarin ya auku ne a kudancin Lubumbashi.

Gwamnan Gunduman Katanga Moise Katumbi, wanda ya gaskata lamarin, inda yake fadin cewa mutane 7 na tsare, yayin da wasu mutun biyar sun bada kansu lokacin da ‘yan-sanda suka yi masu kofar rago.

An cinna wuta cikin tashoshin zabe uku dake Yammacin yankin Kasai, yayin da aka jikata daya daga cikin masu saka ido kan zabe, kamar yadda wata kungiya mai saka dio kan zabe ta kasar ta tabbatar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.