An Samu jinkirin sakamakon zabe a Congo
Hukumar Zabe a kasar Jamhuriyar Demokradiyar Congo, ta jinkirta bada sakamakon zaben kasar da hukuamr ta yi alkalin sanarwa a jiya, sa’oi 48 bayan kammala zaben saboda abinda ta kira matsalolin da fuskanta.
Wallafawa ranar:
Sakamakon da hukumar ta bayar jiya, ya nuna cewar shugaba Joseph Kabila na da kashi 46, yayin da Etienne Tshisekedi yana da kashi 36, daga kashi biyu bisa uku na kuri’un da aka kirga, sai dai ana fargabar tashin hankali.
A lokacin da yake ganawa da kamfanin Dillacin labaran Reuters, kakakin hukumar zaben kasar Laurent Ndaye yace akwai akwai sauran sakamakon da basu samu ba daga wasu mazabu kuma hakan ne yasa aka samu tsaikun bayyana sakamakon zaben.
Sai dai ‘Yan adawa sun ce zasu yi watsi da sakamakon zaben bayan nuna shugaba Kabila ne kan gaba, Al’amarin da ke iya jefa kasar cikin rikici.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu