Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Congo

Rikici ya barke kafin bayyana sakamakon zabe a Congo

Rikici ya barke a kasar Jamhuriyar Demokradiyar Congo, inda aka yi arangama tsakanin masu zanga-zanga da ‘Yan Sanda, ya yin da jami’an diflomasiya ke kokarin kwantar da hankali, kafin bada kammalallen sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a makon jiya.

Magoya bayan  Etienne Tshisekedi,a birnin Kinshasa.
Magoya bayan Etienne Tshisekedi,a birnin Kinshasa. REUTERS/Finbarr O'Reilly
Talla

‘Yan Sanda sun yi ta amfani da hayaki mai sa hawaye kan ‘Yan adawa a Kinshasa, yayin da aka yi ta jin amon bindiga a wani gari da ke yammacin kasar, yankin da ‘Yan adawan ke da rinjaye, bayan Gwamnati ta rufe gidajen rediyo da talabijin.

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya a kasar, ya jagorancin takwarorinsa don ganawa da shugaba Joseph Kabila da abokin takararsa, Etienne Tshisekedi, domin kwantar da hankalin magoya bayansu.

Sakamakon zaben farko da aka fitar kashi 60 ya nuna shugaba Joseph Kabila ne ke kan gaba da kashi 46 na kuri’un da aka kada. Abokin hamayyarsa kuma Tshisekedi ya samu kuri’u kashi 36 matakin da ‘yan adawa suka ce zasu bijerewa sakamakon zaben.

Hukumar kare hakkin Bil’adama ta Human right Watch tace Akalla mutane 18 ne suka mutu sakamakon rikicin zaben.

Wannan shi ne zabe na farko da gwamnatin Farar hula ta gudanar tun bayan kawo karshen yakin basasa a shekarar 2003.

Yanzu haka kuma Akalla ‘Yan kasar Jamhuriyar demokradiyar Congo 3,000 suka tsere daga birnin Kinshasa zuwa Congo Brazaville, don kaucewa tashin hankalin zabe.

Wani jami’in shige da fice na kasar Congo, ya shaidawa Ministan cikin gidan kasar, cewar mutane da suka tsallaka zuwa kasar ranakun asabar da lahadi, sun zarce 3,000.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.