Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Congo

‘Yan sanda sun amsa kashe mutane 4 a jamhuriyyar Congo

Shugaban rundunar ‘Yan sanda a kasar Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ya shaidawa manema labarai cewa ‘Yan sanda sun kashe mutane hudu a rikicin siyarar kasar da ya biyo bayan zaben shugaban kasa.  

Magoya bayan  Etienne Tshisekedi, a birnin Kinshasa sun yi arangama da 'Yan sanda
Magoya bayan Etienne Tshisekedi, a birnin Kinshasa sun yi arangama da 'Yan sanda Daniel Finnan
Talla

Mista Charles Bisengimana, lokacin da yake kokarin mayar da martani kan zargin ‘Yan sanda wajen kwasar ganima da sace kayan mutane, a cewarsa cikin ‘yan sanda akwai ‘yayan banza da suka aikata laifin bude wuta ga gungun masu zanga-zanga.

Mista Bisengimana yace a ranar Juma’a da ranar Assabar ne wasu ‘yan sanda suka bude wuta inda suka kashe mutane hudu nan take. Sai dai yace wadanda suka mutu barayi ne da ke kokarin kwasar ganima.

Kungiyar kare hakkin Bil’adama ta Human Right watch tace tana samun rehotannin cewa ‘Yan sanda na ci gaba da cafke mutane tare da jin karar bindigogi a birnin Kinshasa.

Kakakin kungiyar Van Woudenberg ta shaidawa RFI cewa yana da wahala ayi hasashen lokacin kawo karshen rikicin a cikin kasar.

A jiya lahadi dakarun Sojin kasar da dakarun kwantar da zaman Lafiya na Majalisar Dunkin Duniya sun yi kokarin sauya al’amurra a yankin Gombe birnin Kinshasa.

Bayan sanar da sakamakon zaben, Madugu adawa na Jam’iyyar UDPS Etienne Tskisekedi ya bayyana wa magoya bayansa shi ne shugaban kasa tare da bada kwarin gwiwa ga magoya bayansa na kalubalantar sakamakon zaben.

Sakamakon da hukumar zaben ta fitar, an bayyana Joseph Kabila matsayin wanda ya lashe zaben da kashi 49 na kuri’un da aka kada bayan samun tsaikun sakamakon zaben.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.