Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Congo

Tshisekedi ya jaddada matsayinsa na Shugabancin kasar Jamhuriyyar Congo

Shugaban ‘Yan adawar kasar Jamhuriyar Demokradiyar Congo, Etienne Tshisekedi, ya sake jaddada cewar, shi ne zababben shugaban kasa, kuma zai karbi rantsuwar kama aiki a cikin wannan makon, ikrarin da ya sake jefa kasar cikin rudani.

Madugun Adawar kasar Jamhuriyyar Congo Etienne Tshisekedi tare da tawagar shi sun tunkari filin saukar jirgi na N'Djili a birnin Kinshasa
Madugun Adawar kasar Jamhuriyyar Congo Etienne Tshisekedi tare da tawagar shi sun tunkari filin saukar jirgi na N'Djili a birnin Kinshasa Reuters/Finbarr O'Reilly
Talla

Yayin da yake jawabi, zaune a gaban tutar kasar, kuma kewaye da magoya bayansa sama da 200, Tshisekedi yace yana gabatar da jawabin ne a matsayin zababben shugaban kasa, domin a ranar juma’a mai zuwa, ne zai karbi rantsuwar kama aiki a filin kwallon kasar.

Sakataren Jam’iyyar shugaba kabila, Aubin Minaku, ya bayana matakin a matsayin mafarki.

Etienne Tshisekedi ya yi kiran cafke shugaban kasar Joseph Kabila a duk inda yake a cikin kasar.

A cewarsa duk wanda ya kamo Kabila zai karbi kyauta, tare da kiran Jami’an tsaron kasar amincewa da umurnin shi.

Da farko an yi hasashen zaben shugaban kasar da aka gudanar zai daidaita al’amurra amma kuma an samu mutuwar mutane kimanin 20 sakamakon rikicin da ya biyo bayan zaben.

Wakilan kasashen Duniya da suka kai ziyara kasar domin ganin yadda zaben ya gudana, sun tabbatar da samun kura-kurai tare da tabka magudi, sai dai hukumar zaben kasar tace kura-kuran da aka samu basu shafi sakamakon zaben ba.

Hukumar zaben ta bayyana Kabila a matsayin wanda ya lashe zaben da kashi 46 na kuri’un da aka kada, abokin hamayyarsa kuma Tshisekedi ya samu yawan kuri’u kashi 32, sakamakon zaben da ya yi watsi da shi.

Kabila wanda ya gaji Mahaifinsa bayan kashe shi a shekarar 2001, ya amsa samun kura-kurai a zaben, sai dai yace sahihancin sakamakon zaben abu ne da bai dace a nuna shakku a kai ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.