An sami tsohon mataimakin shugaban DRC da hannu a laifukan yaki
Kotun hukunta manyan laifukan yaki ta ICC a yau litinin ta sami tsohon mataimakin shugaban kasa a Jamhuriyar Demokradiyar Congo Jean-Pierre Bemba da laifin yin sakaci har soji suka sami damar yiwa mata fyade da kisa a Afrika ta Tsakiya
Wallafawa ranar:
Alkalin kotun ICC Sylvia Steiner, a lokacin da yake yanke hukunci yace Bemba ya ki hukunta sojan kungiyarsa ta Movement for the Liberation of Congo, a lokacin da suke ayyukan asha a kasa makwabciyarsu.
Bemba dai ya tafaka kuskure ganin yadda dakarun dake karkashin kungiyarsa suka yi ta yiwa mata fyade da kuma kisan mutane na ba gaira ba dalili inji ICC ba tare da yayi kokarin hanasu ba.
Wannan dai shine karo na farko da kotun ta sami wani jami’in gwamnati babba da alhakin laifin sojan dake karkashinsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu