Isa ga babban shafi
DRC Congo

Hanyar kawo karshen yakin DRC Congo

An sake komawa kan teburin tattaunawa tsakanin gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyar Congo da kungiyar ‘yan tawaye ta M23, domin neman hanyar kawo karshen rikicin da ya addabi kasar.

Wasu daga cikin 'Yan tawayen kungiyar M23 a tautaunawa  na  Birni  Kampala.
Wasu daga cikin 'Yan tawayen kungiyar M23 a tautaunawa na Birni Kampala. AFP PHOTO/ Isaac Kasamani
Talla

A karon farko, bangaren gwamnati da na ‘yan tawayen za su hadu, tun bayan rushewar tattaunawar da aka fara a watan Mayun da ya gabata,
Lamarin da ya haifar da barkewar sabon fada tsakanin bangarorin biyu inda dakarun kasar dake samun goyon bayan dakarun Majalisar Dinkin Duniya suka far ma ‘Yan tawayen.
A makon da ya gabata ,kasashen yankin Great Lakes suka saka kwana uku na wa’adin tattaunawar wanda ya wuce a shekaran jiya litinin.
Amma a yanzu hakka an fara wannan sabon zama a bayan fagen, wanda Ministan tsaron kasar Uganda Crispus Kiyonga ke jagoranta a matsayin mai shiga tsakani inda kuma ake sa ran za a kwashe makwanni biyu ana yi.
Ko wanan tattaunawar za ta cimma ruwa ganin yadda yukurin da aka yi a baya ke samun cikas.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.