Isa ga babban shafi
DRC Congo-Rwanda-Uganda

Babban jami’in Sojin kasar Congo da mabiyansa 30 sun koma cikin ‘yan tawayen M23

Wani babban Jami'in kanar a cikin sojin kasar Jamhuriyar Demokradiyar Congo tare da mukarrabansa su 30 sun koma bangaren ‘yan tawayen M23 dake gwagwarmaya a kasar.

Bertrand Bisimwa, daya koma a cikin 'yan tawaye
Bertrand Bisimwa, daya koma a cikin 'yan tawaye REUTERS/James Akena
Talla

Rahotanni sun nuna cewa Kanar Richard Bisamza na hanyarsa ta zuwa wani aiki ne a wani sansanin soji inda ya yi amfani da damar ya tsere bangaren ‘yan tawayen.

Sai dai rundunar sojin kasar ta ce ba ta yi mamaki da hakan da Kanar Bisamza ya yi ba tana mai jaddada cewa canza shekarsa baza ta kawo gibi a rundunar sojin ba kasar ba.

Bisamza wanda ke a bangaren kabilar Tutsi dai na tafiya ne akan hanyarsa ta zuwa wani aiki da aka sa shi a yankin Lardin Kivu zuwa Kinshasa, kawai ya balle zuwa wajen ‘yan tawaye tare da wasu jami’an Soji 30.

Majalisar dunkin Duniya dai na zargin kasashen Ruwanda da Uganda da taimakawa ayukan ‘yan tawaye, inda su kuma ke zargin kawunan su kan wannan al’amari na ‘yan tawaye da yaki ci yaki cinyewa.

Kabilun Hutu da Tutsi dai manya ne a Gabashin Afruka kuma sunada dadadden Tarihin rashin jituwa a tsakanin su.

Ko a shekarar 1994 ma Hutu masu rinjaye sun kashe akalla ‘yan kabilar Tutsi Dubu Dari Takwas 800,000 a wani mummunan fadan da aka tafka a tsakanin su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.