Isa ga babban shafi
DRC Congo-Rwanda-Uganda

‘Yan tawayen M23 sun janye daga fafatawar da su ke yi da gwamnatin Congo

‘Yan tawayen Jamhuriyar Demokradiyar Congo sun sanar da janyewa daga fafatawar da suke yi da sojojin Gwamnati masu samun goyan bayan dakarun Majalisar Dinkin Duniya.

Wasu daga cikin 'Yan tawayen kungiyar M23 a Jamhuriyar Demokradiyar Congo
Wasu daga cikin 'Yan tawayen kungiyar M23 a Jamhuriyar Demokradiyar Congo REUTERS/James Akena
Talla

Wannan janyewa da ‘yan tawayen suka yin a zuwa ne a dai dai lokacin da makwabciyar Congo, wato Rwanda ta yi watsi da zargin ad ake yi na cewa dakarunta basa yunkurin dakile rikicin dake ci gaba da kazancewa.

An da kwashe kwanaki ana fafatawa tsakanin bangarorin biyu, inda ake amfani da muggan makamai, yayin da ake zargin sojojin Gwamnatin Rwanda da taimakawa ‘yan tawayen.

Hukumomi a Kigali, babban birnin Rwanda sun musanta zargin dake cewa sun tallafawa ‘yan tawayen na M23, wadanda mafi aksarinsu ‘yan kabilar Tutsi ne da suka tsere daga cikin dakarun kasar Congo.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.