Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Congo

An yi bata kashi tsakanin ‘Yan tawayen M23 da dakarun Congo

An kashe wani Sojan Majalisar Dinkin Duniya wata musayar wuta da aka yi tsakanin dakarun Congo da ‘Yan tawayen M23 a gabacin kasar kusa da garin Goma. Mutane uku ne suka jikkata Yayin da Jirage masu saukar ungulu mallakar dakarun Majalisar Dinkin Duniya, suka kai hari kan ‘Yan Tawayen.

Sansanin Dakarun Congo a kauyen Kibati kusa da garin Goma inda suke fafatawa da 'Yan tawayen M23
Sansanin Dakarun Congo a kauyen Kibati kusa da garin Goma inda suke fafatawa da 'Yan tawayen M23 REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

Dakarun MDD akalla 3000 da aka sabunta yarjejeniyar da ke ba su damar kare fararen hula da kuma tarwatsa kungiyoyi masu dauke da makamai a kasar ne suka far ma ‘Yan Tawayen M23 da suka yi wa garin Goma kawanya.

Mai magana da yawun dakarun Majalisar Laftan ; Kanal Olivier Hamuli ya tabbatar da wannan harin da cewa dakarun sun mara wa sojin kasar baya da karfin gaske, inda ya ce a halin yanzu ana musanyar wuta a arewacin garin Goma domin kwace yankunan da ke karkashin ikon ‘Yan tawayen.

A shekara ta 2012 ‘Yan Tawayen M23 suka shiga garin Goma kuma yin hakan ya sa aka koma teburin sasantawa da su amma hakan bai kawo karshen rikicin kasar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.