Isa ga babban shafi
Congo Kinshasa

An dage babban zaben kasar Congo sai 2017

Hukumomi a kasar Congo sun sanar da jinkirta babban zaben kasar Congo har sai watan bakwai na shekara ta 2017, wanda zai baiwa shugaba Joseph Kabila damar zarcewa da mulki sabanin waadinsa na watan Disamba dake tafe. 

Shugaban Congo Joseph Kabila
Shugaban Congo Joseph Kabila AFP PHOTO / CARL DE SOUZA
Talla

Hukumar zabe ta fadi a Kinsasha cewa karancin kudade da za’ayi rajistan masu jefa kuri'u na daga cikin dalilan da suka sa ala tilas a jinkirta wannan zabe.

Masu lura da lamurran kasar na ganin wannan mataki zai kara harzuka ‘yan adawa wadanda tun kafin wannan lokaci suke bore saboda jan kafa da ake yi gameda zaben.

Wasu da dama aka kashe, wasu kuma na tsare hannun jamian tsaro.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.