Isa ga babban shafi
DRC

Faransa ta bayyana damuwar ta kan rikici a Jamhuriyar Congo

Kasar Faransa ta bayyana damuwar ta kan halin da ake ciki a Jamhuriyar Demokradiyar Congo, inda ta bukaci shugaba Joseph Kabila da ya gabatar da shirin gudanar da zaben kasar.

'Yan sanda na arangama da masu zanga-zanga a Congo
'Yan sanda na arangama da masu zanga-zanga a Congo Charly Kasereka / AFPTV / AFP
Talla

Ministan harkokin wajen kasar Jean-Marc Ayraul ya bayyana halin da Congo ke ciki a matsayin mai tattare da hadari, inda ya yi kira ga shugaba Kabila da ya mutunta kundin tsarin mulkin kasar.

Akalla mutane 17 aka kashe a Kinshasa sakamakon aramagamar da akayi tsakanin jami’an tsaro da 'Yan adawa.

A watan Disamba wa’adin Shugaba Kabila ke cika, kuma kundin tsarin mulkin kasar bai ba shi damar sake tsayawa takara ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.