Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Demokradiyar Congo

Kabila ya kulla yarjejeniya da 'yan adawa kan Zabe

Shugaban Kasar Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo Joseph Kabila ya kulla yarjejeniya da wani sashe na 'yan adawar kasar kan yadda za a gudanar da zabubuka masu zuwa sakamakon tsaikon da aka samu.

Shugaban kasar Jamhuriyar Demokradiyar Congo  Joseph Kabila
Shugaban kasar Jamhuriyar Demokradiyar Congo Joseph Kabila REUTERS/Kenny Katombe
Talla

Bangarorin biyu sun amince da shirin gudanar da zaben shugaban kasa da na 'Yan Majalisu, yayin da za a gudanar da zaben Yankuna da na kananan hukumomi kuma tare.

Ministan shari’a Alexis Thambwe Mwamba da Vital Kamerhe daga \yan adawan sun tabbatar da yarjejeniyar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.