Isa ga babban shafi
Dr Congo

Ana cigaba da zanga zanga a Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo

A Kinshasha dake babban birnin Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ana cigaba da dauki ba dadi tsakanin jami’an tsaro da masu zanga- zanga nuna adawa da matakin shugaban kasar Joseph Kabila na kin bada hadin kai domin a gudanar da babban zaben kasar.

Masu zanga zangar adawa da Gwamnatin Josep Kabila a jamhuriyar demokradiyyar Congo
Masu zanga zangar adawa da Gwamnatin Josep Kabila a jamhuriyar demokradiyyar Congo REUTERS/Kenny Katombe
Talla

A yau talata an bayyana cewa masu bore sun cinawa wasu cibiyoyin jam’iyyun adawa uku huta, Felix Tshisekedi magatakarda na jam’iyyar dake adawa da Shugaban kasar UDPS da babbar murya ya tabbatar da cewa gwamnatin kasar na da hannu a wannan hari da wasu mutane suka kai wa Shalkwatar yan siyasa masu adawa da wannan Gwamnati.

Sheidu gani da ido sun kuma tabbatarwa kamfanin dilancin labaren faransa da cewa an hango gawarwakin mutane a wasu wurare cikin garin yayinda aka cinawa wasu gawarwakin huta.
An adai bayyana cewa akala mutane 37 ne suka rasa rayyukan su a cikin wannan rikici zuwa yau.

Bangarorin kama daga Gwamnati dama yan adawa kowa na zargin juna da tada zaune tsaye,inda a wata sanarwa daga ministan cikin gidan kasar yayi kira zuwa mutan kasar da cewa doka zata yi aiki a kai kuma hukumomin sun umurci jami’an tsaro na gani sun maida hankali wajen tabbatar da doka da oda a wasu sassa na babban birnin kasar Kinshasha.

Ma su sa ido dama wasu kungiyoyin kare hakin bil adam suna ta kira zuwa Gwamnatin na gani ta saurari koken yan kasar cikin ruwan sanyi wata hanyar kaucewa duk wani batun zubar da jini.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.